Spread the love

Gwamnatin Jihar Sokoto ta dakatar da Feshin maganin Sauro na miliyan Takwas da Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya kaddamar domin magance Maleriya a yankin mazabarsa.

Sanata Wamakko ya kaddamar da aikin a ranar Laraba da ta gabata.

Ma’aikatar lafiya ta fitar da bayani dakatar da aikin a jiya Alhamis ta hannun Babban Daraktan hukumar kawar da maleriya Muslim Adamu Gobir, amadadin kwamishinan lafiya na jihar Sokoto, an dakatar da aikin ne domin amfanin jama’a.

Ya ce an yi amfani da sinadaran da ba a sani ba a wajen feshin kuma ba da izinin ma’aikatar lafiya aka yi ba

“Ba zai yi wu mutum ya dauki matakin watsa sinadarai ba tare da sanin ma’aikatar lafiya ba domin ta duba ta ba da izini gudun kar a sanya rayuwar mutane cikin hadari.”

Sinadaran ba su da inganci suna iya zama guba da suke iya taba lafiyar mutanen da ba su ji ba su gani ba. Domin kariyar lafiyar mutane ba wani mutum ko gungun jama’a da zai rika daukar sinadarai yana watsawa ga mutane ba tare da izinin ma’aikar lafiya ko wata hukuma ba” a cewarsa.

Ya ce kan haka ma’aikatar lafiya tare da hadin kan ma’aikatar muhali sun kaddamar da mutane ‘duba gari’ su zagaya duk wani mutum da suka gani yana feshi ba da izini ba su kama shi su hannunta shi ga jami’an tsaro don a hukunta shi.


Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya Bayyana Cewa , Shirin Feshin Maganin hana kamuwa da Cizon Sauro da ya dauki Nauyi a Kwaryar Sokoto, da Manufar taimakawa Jama’ar Mazabarsa ne kawai.
ya ce, Matsayinsa, na Zabbaben, Sanata ba zai yi, Wani abu da Zai Cutar da Jama’arsa ba.
‘Wannan Shirin na da Zimmar Kamawa Kokarin Gwamnati ta, Hanyar Yakar Zazzabin Cizon Sauro ga dimbin al’ummar Wannan Gundumar’

Ya ce Shirin Feshin nada Kudurin ganin an rage Matsalar “Wannan bai da wata cuta ga Wadan da ake yi wa. in ji shi.
Sanata Wamakko ya Bayyana Cewa,”Ina da Yakinin Cewa Gwamnatin Jihar Sakkwato, ba Za ta Hana Cigaba da Wannan Shirin ba, amma dai idan tana ganin za ta iya Cigaba da aikin, to, sai mu Jingine namu , ta ci gaba da yi.
Sanata ya yi wadan nan kalamai ne ta hannumataimaki na musamman nasa kan harkokin manema labarai Malam Bashir Rabe Mani, Dan Masanin Mani. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *