Spread the love

Hukumar kula da jami’o’i ta kasa ta aminta jami’ar Usman Danfodiyo dake Sokoto ta kirkiro tsangayar koyar da ilmin kimiyar hakora.

shugaban jami’ar Farfesa Suleiman Lawal Bilbis ne ya sanar da hakan a lokacin da ya jagoranci shugabannin jami’ar a ziyarar ban girma da suka kaiwa Gwamna Aminu Waziri Tambuwal fadar gwamnatin Sokoto.

Shugaban ya ce kan wannan amincewa da suka samu jami’ar za ta fara karatun digiri a wannan fanni a shekarar karatu ta 2019/2020.

Farfesa Bilbis ya kara da cewar jami’ar na jiran amincewa kan fara karatun aikin jarida da wasu fannoni guda uku.

Ya godewa gwamnatin jiha kan gudunmuwar da take ba jami’ar.

Ya ce nan ba da jimawa ba hukumar jami’ar za ta fara ginar zagaye fili mallakar jami’ar gaba daya.

Gwamna Tambuwal ya godewa shugabannin makarantar kan ziyarar da aka kawo masa, ya yi alkawalin cigaba da hada kai da shugabanin makarantar a cigaban ilmi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *