Spread the love

Shugaban Kauye ko Hakimi na Wurma a karamar hikumar Kurfi ta jihar Katsina, Alhaji Mustafa Muhammad ya ba da labarin yanda daruruwan mahara suka shigo kauyensu suka save mutum 49.

“Maharan sun zo da bindigogi sai dai ba su kashe kowa ba amma sun tafi da mutum 49”

An saki 11 an kuma fadamin an saki mutum daya

Muna kira ga Gwamnan Katsina da jami’an tsaro su taimaka muna a kare mu ga maharan, su bar kawo mana hari.

Badamasi Wurma Wanda aka tafi da matarsa da yaransa uku ya ce ina tare da abokaina mu shida da misalin 11:30 na dare muka ji harbi ta ko’ina kowa ya gudu ya tseratar da rayuwarsa ba mu sake ganin juna ba sai da safe maharan sun kai 300. A cewarsa.

Bayan na tafi gida ne da safe na samu gidan a balle na shiga ciki an dauken duk wani abu na amfani sun tafi da matata.

Diyana mata suna cikin mutum 45 da suka tafi da su, amma dayan tana cikin wadan da suka dawo.

DPO da motarsu ta rika sintiri a wurin bayan maharan sun tafiyarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *