Spread the love

Sheikh Bala Lau ya halarci taro a kasar Turkey

Daga Ibrahim Baba Suleiman.

Shugaban IZALA Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, Da sakataren kungiyar Sheikh Dr. Muhammad Kabir Haruna Gombe, sun halarci Taro a birnin Istanbul na kasar turkey kan “Takaful Insurance” a tsarin musulunci.

Cibiyar hulda na Al Huda Islamic banking da sauran cibiyoyi na hada hadan kasuwanci a tsarin musulunci, su suka shirya taron, kamar yadda suke suke shiryawa lokaci bayan lokaci a baya. In baku manta ba, a bara sun shirya taron ne a birnin Dubai na kasar UAE, a wannan karo kuma suka shirya a kasar Turkey, kuma kasashe Da dama irin su, Pakistan, Bosnia-herzegovina, Saudi Arabia, Egypt, Turkey, Sudan, Senegal, Nigeria, Ethopia, Malesia, Indonesia, India da sauransu.

A karshe cibiyar Al-Huda Islamic banking ta karrama manyan Malaman na kungiyar ta JIBWIS, Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, da Shaikh Muhammad Kabir Haruna Gombe.

Allah ya kara girma da daukaka, yasa adace da daidai akan ayyukan da akeyi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *