Spread the love

Kasuwanci ya yi matukar wuya a bododin kasa na tarayyar Nijeriya yanda jami’an Kwastam suka tsaurara matakan tsaro na hana shiga da fice.

Wannan abin yana faruwa ne sati daya bayan da aka rage zirga zirgar kasuwanci a bodar Lavas kan abin da ya shafi harkar tsaro.

Hukumar Kwastam ta ce wannan mataki yana daga cikin matakan da suke dauka na kare kasa.

Jami’in Hulda da jama’a mataimakin Kwanturola Joseph Attah ya fitar da bayani kan lamarin iyakokin ne na kasa gaba daya.

Wannan matakin da aka dauka ya kawo kasuwanci ya tsaya cik mutane sun fara kokawa kan lamarin.

Attah ya ce bododin ba rufe su aka yi ba kamar yadda wasu ke fadi abin da a gaskiyar lamarin ba a rufe ba jami’an tsaro ne ke aikinsu na tabbatar komi na tafiya lafiya.

Duk iyakokin da manema labarai suka ziyarta za su samu a rufe suke ba shiga ba fita duk da jami’an Kwastam sun ce ba a rufe ba.

Motoci ne a baking wata boda an hana su wucewa shiga jamhuriyar Nijar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *