Spread the love

Mahara dauke da muggan makamai sun kashe mutum uku sun save mutane da damage kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Wani direban motar gaya da ya samu ya tsare dakyar ne ya sanar da jaridar daily trust cewa Maharan rufe hanya suka yi gaba daya daidai kamfanin Olam da misalin karfe 5:30 na yamma.

‘Sun kashe mutum uku sun sace mutane da dama da suka tare hanya suka rika harbin ababen hawan mutane, sun tafi da mutane da dama cikin daji.

‘Na ga gawar mutum uku da motoci shida gefen hanya kofofinsu a bude. Bayan maharan sun wuce da minti 30 sojoji suka zo wurin. Ina cikin direbobin da suka tsalke rijiya da baya tare da fasinjojina da na dauko Daga Abuja’ in ji Adamu.

Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta Kaduna DSP Yakubu Sabo ya nemi aba shi lokaci ya binciki DPO da ke kula da yankin, amma har lokacin bugs labarin bai ce komai ba.

Dalibai ne a jami’ar Ahmadu Bello suna karatun shari’a, suna cikin wadan da aka yi garkuwa da su

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *