Spread the love

SOYAYYAR KARYA TA ‘YAN ZAMANI

Daga Fauziya D. Suleiman

Yaran yanzu don ana soyayya ba abun kunya ba ne su rungumi juna a gaban kawaye da abokai wani lokacin har da iyaye ma, haka nan gurin taron bukukuwa a gaban iyaye za su rungumi juna har da sumbata ana ihu da tafi.

To ku sani wallahi wannan shi ne tushen rashin albarka a aure, an gama watsar da duk albarkar da mutumcin a titi, me ku ke tsammanin zai faru idan an yi auran?

Irin wannan aurarraki su ne ake caka wuka, su ne ake dukan abokin aure, shi ne ake zagin juna har da iyaye, shi ne ba a ganin darajar juna, shi ne ake zargin juna kullum cikin rigimar kar mace ta rike babbar waya shi kuma miji yana ta boyon waya da saka ‘password’ masu zafi, shi ne bai cika shekara ko watanni ke fita daga ran maauratan har ya mutu cikin kankanin lokaci.

To wallahi ku sani idan har ba mu gyara tarbiyyarmu da ta yayanmu ba, Allah ba zai aiko mala’iku su gyara mana ba, za mu ci gaba da zama cikin rudu da rudani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *