Spread the love

Hukumar Kula da Jami’o’i ta kasa ta baiwa shugaban Kwamitin kula da lamurran tsaro na Majalisar Dattawa ta kasa, sanata Aliyu Magatakarda Wamakko damar kafa Jami’ar kimiyya da fasaha mai zaman kanta ta farko mai suna “Jami’ar kimiyya ta Arewa Maso Yamma a sakkwato”.

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi takardun cikewa guda goma na shirye-shiryen fara kafa jami’ar mai zaman kanta mai suna “Jami’ar Kimiyya da fasaha ta Arewa maso Yamma”, a can Shalkwatar hukumar ta kasa dake Abuja a Ranar Alhamis da ta gabata.

Sarkin Yamman Sokoto, ya bayyana cewa daukacin yankin na Arewa maso Yamma, babu Jami’a guda a hadun mai zaman kanta wadda zata kula da samar da gurabun karatu ga dimbin Daliban dake neman ilimi a Jami’o’i

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya bayyana cewa, Allah cikin ikon sa, Ya bashi damar Kammala kariyar aikin sa na Digiri ta uku, waton Digirin Digirgir a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, ba domin neman wani aikin Jami’a ba a nan gaba sai dai domin Ganin manyan gobe (Matasa) sun bi sahun magabata ta neman ilimi ba kama hannun yaro.

Ya kara bayyana godiyar sa ga Mahukuntan Hukumar mai kula da Jami’o’i ta kasa kan goyon bayan su ga Gwamnatin sa na samun kafa Jami’a malakkar Gwamnatin Jihar sokoto a lokacin yana Gwamnan Jihar sokoto.

Sarkin Yamman sokoto, a jawabin da jami’in hulda da jama’a da manema labarai nasa Bashir Rabe Mani ya bayyana cewa ya samar da ilimi kyauta a lokacin yana Gwamna a matakai daban-daban har tsawon karewar Wa’adin mulkin sa.

Tun da farin da yake magantawa, Sakataren Zartarwar Hukumar, Farfesa Abubakar Rasheed, ya nuna damuwar sa na rashin Jami’a mai zaman kanta a Jihar sokoto dama yankin Arewa maso Yamma domin kula da dimbin bukatar dake akwai na samar da gurabun karatu ga Jama’ar dake bukatar zuwa Jami’o’i kuma suna da kishirwar samun gurabun karatun amma abin ya faskara.

Daga nan, sai ya yabawa Mai girma Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko kan tunanin kafa Jami’ar domin ganin an daga Martabar Ilimi a yankin na Arewa Maso Yamma, da daukacin Kasa baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *