Spread the love

HASSADAR DA KE TSAKANIN TALAKA DA MAI ARZIKI RASHIN ADALCIN MAWADATA NE~Dino Melaye

Dino Melaye ya fadi haka a cikin wata sabuwar hira da yayi yace kowani Talaka yana da ‘yanci kamar kowani dan Najeriya.

A wani faifan bidiyo da ya sanya a Shafinshi na Twitter Dino ya yi nuni da cewa talakawa da matasa ba su farin ciki da yadda shugabannin ke tafiyar da al’amuran su, duk da cewa sun zabe su.

Ya ce, “Shugabanni dole ne su samar da yanayi mai kyau ga matasa, bai kamata ba ace wasu ‘yan Najeriya suna da damar rike kashi 95% wasu kuma 5% talakawa da ba’ yan boko ba ne”

Sanatan ya kara da cewa yaki zai iya ballewa tsakanin talakawa da attajirai. A lokacin da babu wani daga cikin Yansiyasa da manyan mutane da zasu sake zama lafiya saboda rashin adalci da sukeyi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *