Spread the love

Dan Kwalllon Nijeriya Abdullahi Shehu Ya Sa An Nemo Masa Wasu Yara Da Ya Ga Suna Sana’ar Gasa Masara Domin Ya Dauki Nauyin Karatunsu

Daga Dan Almajiri

Shahararen dan kwallon kafar ban dan asalin jihar Sakkwato Abdullahi Shehu, mai wasa a Nijeriya da Busassapor dake kasar Turkiya ya tura mu mun je mun yi magana da mahaifin yaran akan zai dauki nauyin karatunsu.

Kasancewar yanzu ana zangon karatu na karshe (Third Term), Abdullahi Shehu ya bada tallafin kudi naira dubu ashirin- ashirin ga kowanne yaro daga cikin yaran domin su kara karfafa sana’ar su ta saida masara.

Ya yi alkawarin da an dawo zangon farko na karatu aka fara bada gurbin shiga makaranta zai sanya su a makaranta kuma ta kudi ba ta gwamnati ba, kuma ya yi alkawarin daukar nauyin karatunsu har su gama sakandire.

Wannan tafiyar mun yi ta ne karkashin jagorancin Shugaban Gidauniyar Abdullahi Shehu (Abdullahi Shehu Foundation) wato Ahmad Tijjani (Andi Coach) tare da shi akwai jami’in hulda da jama’a na Gidauniyar, wato Bello Muhammad Danrabi.

Abdullahi Shehu yadda kake taimakon jama’a da kuma son ganin matasan Sakkwato sun ci gaba, ina rokon Allah Ya saka maka da alkairi Ya kara maka daukaka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *