Spread the love


Shahararren Jarumin Kannywood Kuma Mawaki Yusuf Haruna Funtua Wanda Akafi Sani Da (Baban Cinedu ) Ya Bayyana Cewa Rarara Ne Yake Sawa Shugaban Hukumar Tace FinaFinai Na Kano Ismaila Na’abba Afakallahu Yana Cin Mutuncin Mutane A Kannywood.

Kamar Yadda Jaridar Amintacciya Ta Wallafa Videon Sa Inda Yake Cewa Abinda Ke Faruwa Abin Dariya Ne Wai Yaro Ya Tsinci Hakori.

Yace Afakallahu Kasan Nasanka Ba Sanin Shanu Ba Inma Kaiwa Wasu Mu Karyanka Wallahi Munsanka Ka Sanmu.

Yace Yanzu Kai Aikin Da kake yi Aikin Rarara Kake yi Idan Rarara Yana Da Matsala Da Wani. Daya Nuna shi da Baki Saika Kamashi Ko Ku Rike Masa Film Kamar Yadda Kaiwa Bulama Saboda Rarara Yanada Matsala Dashi Sai Ka Rike Masa Film Tin Ana Taya Film Dinsa Miliyan Uku Da Rabi Har Yadawo Dubu 600 Sannan Kuka Sakar Masa Ba Laifin Komai Saboda Ku Karya Masa Jari.

Yanzu Sunusi Oscar Yaje Yagama Darektin Wakoki Kuma Na APC Dukda Dai Ku APCn Dakuke Iya Kano Kukeyi Dama A Kano Ungulu Dakan Zabone Kukeyi Oscar Yaje Yagama Aiki Yadawo Saboda Ba Wanda Kuke Shiri Dashi Bane Kun Tura An Kamashi – Inji Baban Cinedu

Kamar Dai Yadda Kuka Sani Baban Cinedu Shine Babban Abokin Wakar Rarara Saidai A Wannan Karon Yace Komai Zai Faru Saiya Fadi Gaskiya Rarara Ne kesa Aci Mutuncin Mutane A Kannywood Idan Basa Shiri Da Juna

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *