Spread the love

Kotun sauraren karar zabe ta majisar tarayyar Nijeriya ta soke zaben Sanata Dino Melaye Sanata mai wakiltar Kogi ta Gabas.

Dino ya samu kuri’u 85,395 ya kayar da abokin karawarsa na APC Sam Adeyemi wanda ya samu kuri’a 66,902 kan haka ya kalubalanci zaben don yana zargin aringizo da yin zabe fiye da ka’ida da sabawa dokokin zabe.

Alkalan su uku karkashin jagorancin Alkali A.O Chijioke sun yarda da korafin mai kara sun ce a sake zaben a mazabun gaba daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *