Spread the love

Majalisar tattalin arziki ta kasa ta aminta a kafa kwamitin da zai karbo biliyan 614 bashin da aka baiwa jihohi 35 ban cin Lagos kan su taimaki kasafinsu na kudi.

Wannan yana cikin hukuncin da aka yanke a taron da mataimakin shugaban kasa ya jagoranta zauren fadar shugaban kasa.

Ministar kudi da Kasafi da tsarin kasa Zainab Ahmad ce tare da gwamnan Nasarawa Abdullahi Sule dana Edo Obaseki ta ce majalisar ta aminta da a karbo kudin ga hannun jihohi lokacin dawo da bashi ya yi.

Kudin da aka ba su biliyan 614 ga jihohi 35 kowace jiha ta karbi 17.5.

Majalisa ta yarda a kafa kwamiti daga ciki akwai wakilin gwamnoni da ma’aikatar kudi dana babban bankin kasa domin fitowa da hanyoyin da za a bi wajen fara karbo kudin, kuma CBN ce za a baiwa kudin. A cewarta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *