Spread the love

NEMAN ILMI DA AURE DA HALAYEN MODIBBO KILO

Neman Ilminta

 Modibbo Kilo ta fara karatu a hannun mahaifinta Al}ali Mahmudu kuma gare shi ta yi saukar Al}ur’ani, tun ba ta kai shekara 7 ba. Ta yi tushin wannan karatu ga malamarta Modibbo Fa]imatu wadda ake kira ‘Yar Dije. Mahaifinta Al}ali Mahmuda da Modibbo Fa]imatu sun ci gaba da karantar da ita littattafan sani irin su Usuluddin da Ahlari da Ishmawi da Izziya da Risala da {ur]aba da Lawwali da Sani da kuma Tafsiri. Ta ci gaba da wannan karatu a hannun yayanta malam Shehu Muhtin Sakkwato wanda ta sauke Ishiriniya a hannunsa. Ta yi karatu kuma a hannun malamarta Modibbo Hauwa’u Mammange[1], yayar wani mashahurin malami a Sakkwato Malam Bube da Modibbo Mo’e ]iyar malam Akali wanda ya na}alci Mukhtasar, [2]. Ta yi karatu a hannun mijinta Sarkin Yamman Kware Abdullahi Bayero wanda ya ci gaba da karantar da ita bayan ta aure shi. Ta mai da karatu babbar sana’arta wanda take yi dare da rana, akoyaushe aka same ta ko dai tana ri}e da littafi tana karatu ko tana karantarwa ko tana rubutu, tana kuma da yawan salla da tasbihi.

 Aure Da Iyali

 Da shekara 9 aka yi wa Modibbo Kilo aure. Ta auri Sarkin Yamman Kware Abdullahi Bayero ]an mallam Isa, autan mujaddadi Shehu Usmanu [anfodiyo. Sun yi zaman lafiya kwarai da mijinta har ya kasance yana ce mata anya idan ya mutu kuwa za ta iya aure. (Hira da modibbo Fatima Sarauniya ranar Laraba 4/7/2012) Ta }ara samun ilmi sosai a hannun wannan miji nata har ta zama tana karantarwa a gidansa, amma daga baya }addara ta sa suka rabu saboda al’amari na ilmi da gyara karatu.

Bayan rabuwar aurenta da Sarkin Yamma Abdullahi Bayero, ta auri malam Akwara na shiyar ‘Yola a Sakkwato, malami kuma ]an kasuwa. Daga baya wannan aure ya mutu sanadiyar bu]a muryar da take yi idan tana karatu, daga su ba ta sake yin wani aure ba. (Hira da malam Ibrahim Gandi Junaidu ranar Assabar 26/5/2012) . Modibbo Kilo ba ta ta~a haihuwa ba har ta koma ga mahaliccinta. Modibbo Kilo ta rasu a garin Makka a shekarar 1976.

  Yanayinta Da Halayenta

‘Yan’uwan Modibbo Kilo da wa]anda suka san ta sun bayyana yanayinta suna cewa, ita mutawassi]a ce, ba tsawo can ba, ba kuma gajera ba, tana da doguwar fuska da dogon wuya. Ga kalar jikinta fara ce mai kyaun siffa. Yawancin suturar da take sa wa a lokacin da take  Sakkwato ta dal}e ce mai kalar shu]i-shu]i, tana ]inka babban zani har }asa, ta ]ora wani abu a kanta wanda ake kira Tiggare wanda sai mai ilmi, masani ka]ai ke amfani da shi sannan ta ]ora babban zani a kanta wanda zai rufe ta shifshif.

Mai ]a’a ce ga iyaye da son zumunci kuma mai fa]in gaskiya ce duk yadda al’amari ya kasance. Ta}iyya ce mai tsoron Allah, mai kuma tsentseni ga duniya. Mai kunya ce da kamun kai, ba ta duban maza sai bisa larura, idan kuma tana tafiya }asa-}asa take duba ba ta son ]aga kai.

Tana da yawan kyauta da taimako, ko abu ya zama shi ka]ai ke gare ta, tana iya ba da shi, tana kuma yawan aikawa mutane abinci da sauran abubuwan da Allah Ya hore mata[3]. Modibbo mai fa]in gaskiya ce, saboda fa]in gaskiyarta, duk ‘yan’uwa da abokanta sun san cewa idan ba a son a bayyana wata rashin gaskiya to kada a yi a gaban ta. (Hira da zuriar Al}ali Mahmudu ranar 29/5/2012)

An yi bayanin cewa Modibbo Kilo mai tsaya wa kanta ce, kuma ba ta son haram ba ta cin sa. Dalilin haka ne aka ce da ita da jama’arta mata har gini suke yi a gidanta, su yi ha}on rami su kwa~a }asa su yi gini da kan su. Hakanan suna noma su yi ‘yan shuke-shuke domin amfanin gida. Mutane sukan zolayi mai mata hidima Maryamu Kurma, su ce, “ku mahaukata ne, ku mata ku yi noma da gini da kanku?” Sai ta ce “Moo-moo di dib-bo, ta-ta ce- mu-mu yi -ko- mai ci-ci-ci kin ha-ha laaa lin mu”, wato Modibbo ta ce su yi komai cikin halalinsu. ( Hira da Hajiya Fatima Baba Tafida ranar 4/7/2012)


orce-w�rC��

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *