Spread the love

SHEKARU UKU DA SUKA WUCE NAYI MAGANGANUN SOSAI AKAN MUTUWAR WANI YARO DAYAKE HARKAN WAƘA,
KUMA BANSO NA SAKE MAGANA AKAN HARKAN FILM INDUSTRY BA ƘWATA ƘWATA

Amma dalilin wasu zantuttuka da bayanai dana gani daga Bakin #AdamAzango yayi akan “yana neman Sabbin yan mata da zai saka a harkan film yasa insha Allah zanyi wasu jerangiyar rubuce rubuce akan wadannan mutanen

(1) Ya akayi na tsinci kaina a harkan Industry
(2) Rayuwata a cikin Harkan, da matakan dana taka, shin nima ni dan kuci ku bamu ne? Ko nayi suna sosai?
(3) Wasu dalilai ne suka na bar harkan Film industry cikin Taimakon Allah
(4) In kana so ka shiga harkan Film wasu hanyoyi zaka bi
(5) Shin Harkan film Maza akafi buqata ko maza, wanne yafi samun karbuwa da wuri
(6) Hatsarin dake cikin harkan tun tashin farko a cikin( rukunnan harkan film)
(7) Ya rayuwarka zata kasance kafin kayi suna duniya tasanka
(8) shin yan film mutanen kirki ne kuma wa’azi sukeyi kamar yadda suke cewa
(9) Shin kafin kayi suna akwai wasu matakai daya kamata kabine, kuma akwai wasu abubuwa da ake buqata kayi kafin kayi suna
(10) Meke faruwa a studio, gun location (shooting film) da sauransu
(11) Suwa akafi lalatawa tsakanin maza da mata a harkan
(12) Shin akwai wani mai riqo da addini ko mai tsawatarwa a cikin harkan
(13) illar harkan Film Ga Al’ummar musulmi
(14) daga shiganka harkan me zata fara rabaka dashi
(15) Ya zaka katange ƴaƴanka ƙannenka daga wannan tsinanniyar
(16) Shin kudin industry suna da albarka?
(17) Wace illa suke fesawa yaran mu da matan mu da matasan mu da sauran Al’ummu?
(18) Akwai yan izala a cikin harkan? Ya yan izala suke kallon harkan? Ya yan dariqa da shi’ah suke kallonta? Sannan suwa sukafi yawa?

harkan cikin taimakon Allah

Insha Allahu wadannan bayanan da ma wasu zasu biyo baya insha Allahu

Sannan masu harkan sun sha yimun barazana da turo mun jami’an tsaro da kiran Iyaye na da sauran su, duk domin na dena tona masu asiri tunda na bar harkan yanzu

Amma hakan bazai sanyani na tsorata ba zan yi iya yina dan ganin nayi iya bayanan dana sani dan masu rabin shiriya a cikin su su shiryu

Ina rokon yan uwa su rokamin Allah ya bani ikhalasi ya tsare daga tozarta wani, ya tsareni daga zamiya

Allah ka tabbatar dani Akan dai dai da fadin dai dai kuma! Nayi adalci

Allah ka tsare al’ummar musulmi daga Sharrin Yan Wasan kwaikwayo, Allah ka shiryi masu shiryuwa daga cikinsu
Mu kuma Allah ka tabbatar dani akan dai dai kada na zame na koma cikin wannan jahiliyyar

الحمد لله الذي أنقذنا من حال أهل النار
ونعوذوا بالله من حال أهل النار
اللهم لولا أنت مهتدينا ،اللهم اهدنا فيمن هديت

Usman Abu Abdilrahman
19/8/2019

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *