Spread the love

An kama mutumin da ya hada ‘yan sanda da sojoji fada

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sake kama mutumin nan da ya yi ‘kaurin suna’ wajen garkuwa da mutane mai suna Alhaji Hamisu Bala Wadume.

A wata sanarwa mai dauke da sa-hannun mai magana da yawun rundunar, DCP Frank Mba, rundunar ta ce an kama wanda ake zargin ne ranar Litinin da yamma a maboyarsa da ke kan layin Allo da ke yankin Hotoro a birnin Kano.

Sanarwar ta ce: “Tun ranar 6 ga watan Agusta 2019 rundunar ‘yan sanda take farautar wanda ake zargin bayan da aka samu tsautsayi a Ibi na jihar Taraba.

Wannan al’amari ya yi sanadiyyar kisan gilla ga ‘yan sanda uku da kuma farar hula guda biyu tare da jikkata wasu mutum biyar.”

“Mutumin da ake zargin ya tsere ne daga hannun sojoji bayan sun balle ankwar da ke hannayensa,” In ji sanarwar.

Batun ‘tserewar’ Alhaji Hamisu Bala Wadume ko kuma ‘tseratar’ da shi da ‘yan sanda suke zargin sojojin Najeriya da shi ya tayar da kura a tsakanin sojoji da ‘yan sanda da ma ‘yan Najeriya.

Al’amarin ya kai ga rundunar ‘yan sandan kasar tuhumar sojoji da hada baki da mutumin.

Rundunar ta ‘yan sanda dai ta nemi sojoji su yi mata bayani kan yadda Alhaji Hamisu Bala Wadume ya tsere duk da cewa ya kasance cikin ankwa a kafa da hannu.

‘Yan sanda sun zargi sojojin da harbe jami’ansu wadanda suka kamo mutumin da ake zargi duk kuwa da cewa ‘yan sandan sun bayyana katin shaidar kasancewarsu ‘yan sanda.

Sojoji sun ce mutanen gari ne suka nemi taimakonsu cewa masu satar jama’a sun yi garkuwa da wani kuma da suka tsayar da ‘yan sandan a shingen tsaro da suka kafa, ba su tsaya ba.

Wannan badakala dai ta bayyana irin zaman ‘yan marina da jami’an tsaron Najeriya ke yi da juna musamman a irin yanayin da suke ciki na yaki da ta’addanci da sauran ayyukan bata-gari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *