Spread the love

Mai gabatar da kara gaban kotu Insfekta Adeoye Adesegun ya sanar da kotu wanda ake zargi da ke gabanta ana tuhumar shi da yi wa wata daliba fyade a ranar 31 ga Julin shekarar nan da misalin karfe 6:30 cikin Ikare-Akoko a shingen sojoji.

Adesegun ya ce laifin ya sabawa sashe 357 da hukuncin laifin a sashe na 358 a manyan laifuka cap37 kundi na 1 a dokar jihar Ondo ta Nijeriya 2006.

Babban Alkalin kotun Majistire da ba da umarnin korar sojan dan shekara 33 Sunday Awolola daga aiki kan wannan zargin na yi wa dalibar jami’ar Akungba Akoko, a ci gaba da rike shi gidan yari har sai an samu shawarar doka kan lamarin.

Alkali Mayomi Olanipekun ya ki aminta da sakin sojan sai an samu shawarar shari’a bayan an kore shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *