Spread the love

Jam’iyar PDP da dan takarar shugaban kasarta Atiku Abubakar sun roki kotun sauraren karar shugaban kasa ta soke cincintar Shugaba Buhari ga zaben 23 ga Fabarairu da aka gudanar.

A rubutun daftari na karshe da suka yi jagoran lauyoyin Atiku, Babban lauya Levy Uzoukwu suka nemi hakan a gaban kotu.

Sun nemi Buhari ya gabatar da takardar kammala Firamarinsa ko Sikandare ko ta babban jami’in soja. Da dadewa ina takardun suke da yake ta kuarin ya mallaka da ya fadi a cikin fom CF001.

PDP da Atiku sun ce Buhari bai cika sharadin da sashe na 31(2) a tsarin dokokin zabe ga fom CF001.

Sun nemi Kotun sauraren kara ta ayyana zaben wanda bai inganta ba dake cike da aringizo da ya kasa bin tsarin dokokin zabe na 2010 da tsarin bin zabe na 2019.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *