Abokin fecebook ya sace budurwa a Jos

TA HADU DA SHARRIN KAFOFIN SADA ZUMUNTA

Kimanin Kwanaki Biyar Kenan Da Bacewarta

Wannan yarinya sunanta Sadiya daga garin Jos jihar Pilato, ana cikiyarta, ta bata bat yau wajen kwana biyar.

Ta hadu da wani mutum da suka hadu a dandalin sada zumunta, ya mata alkawari zai zo Jos su gana, ta fita daga gidansu akan zata taro bakon nata, to tun daga wannan lokacin ba’a sake jin duriyarta ba

Kuma tun daga lokacin fitar ta daga gida zata taro bakonta nambar wayoyinta duk a kashe, an nemeta sama da kasa an rasa, kuma ba’a san ta inda suka hadu da mutumin ba balle a fara bincike.

A yanzu dai ‘yan uwanta sun fitar da neman cigiyarta, jama’a sai a taimaka ko da addu’a.

Daga bangaren mu za mu hada ‘yan uwanta da masu bincike a wannan fanni Insha Allah.

Bayan haka ‘yan uwa a yi taka tsantsan, wannan darasi ne gare mu gaba daya, a guji saurin yadda da mutane musamman wadanda aka hadu ta kafofin sada zumunta.

Muna rokon Allah Ya bayyanata cikin aminci Amin.

Daga Datti Assalafiy

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *