Spread the love

Kungiyar masu shirya finafinnai ta jihar Sokoto ta zabi sabbin shugabanni a yau Lahadi

Zaben Wanda shugaban kwamitin shirya zabe Malam Sa’adu Labbo Sokoto ya jagoranta ya bayyana shugabanni da za su ja ragamar kungiyar su 10.

Zaben ya yi armashi an kammala cikin lumana da nishadi ganin ba wata kazamar adawa tsakanin mambobin kungiyar abin da ya kai ga kare zabe ba hamayya da korafi ga kowane mamba.

Bayan kammala zaben sabon Shugaba Bello Shehu Acida ya godewa mambobin kungiyar da suka ba da had in kai har aka samu wannan nasara.

Ya ce zai iyakar kokarinsa ya kawo cigaba a harkar fim ta jihar Sokoto, kofar shi a bude take ga duk wanda zai kawo shawara mai amfani da za ta ciyar da harkar gaba. A cewar Bello Acida.

An zabi Aminu Abdullahi Maigaskiya sakataten kungiya, Alhaji Rabi’u Abdullahi Ma’aji, mataimakiyar Sakatare ya fada kan Halima Mohammed Baba.

Jami’in hulada da jama’a Ibrahim Umar (Walis), Sani Muhammed Mantis ne Sakataten kudi, Odita 1 Shehu Dan Tuni Shagari, Yahaya Bawa Muryala Odita 11.

Kudirat Moshood Sakatariyar shirye-shirye da Fatima Ahmad(Zombi) a matsayin sakatariyar Walwala.

Kungiyar ta yi kokari a wurin kiyaye daidaiton jinsi sabanin sauran kungiyoyi da ke danne mata ba su bari su ma su fito su ba da ta su gudunmuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *