Spread the love

Hukumar Kwastan Ta Kama Kwayar Tiramol Da Kodin Na Sama Da Naira Bilyan Biyar

Ba don Allah ya kai idanun hukumar Kwastam wajen ba, da tuni sun samu nasarar kai muggan kayayyakin zuwa inda matasa za su cutu.

Codeine, Tramadol aka jibge a wata ma’ajiyar kaya dake Oshodi Lagos, kayayyakin da aka kiyasta kudinsu ya haura naira bilyan biyar, inda ake kyautata zaton an yi niyyar shigar da su ne wasu jihohin da ake tsammanin na Arewa, inda nan masu safarar miyagun kwayoyi suka fi turawa da kayansu.

Tuni dai Hukumar Kwastam ta kame kayan gaba dayan su tare da garkame su a dakin ajiyar kaya da aka same su a ciki, sun kuma bazama neman mamallakin muggan kayayyakin da mai mallakar ma’ajiyar da aka samu kayan.

Manyan tirelolin daukar kaya guda ishirin da daya ne shake duk da wadannan miyagun kayan.

JUNGLE JUSTICE ZANYI DA NINE ALKALI….

Idan aka samu mutumin da yayi niyyar cutar da ya’yan wasu wajen siyar musu da wadannan kayan mayen, sai kawai na yanke masa hukuncin shida iyalansa da dukkan yaransa dake aiki karkashinsa, za su shanye dukkan Codeine da Tramadol gaba daya, koda kuwa za su shakara hamsin suna sha, saurin shanyewar su shine dai dai wa’adin da za su yi a kulle.

Daga Rabiu Biyora

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *