Spread the love

 

Hadarin da ke tattare da magungunan  cutar dabbobi ya haifar da tabarbarewar kiyon lafiya a Duniya. Annobar tafi yawa a Afirika ta yamma musamman a Nijeriya a fannin kiyon tsuntsaye.

Magungunan  cutar ana amfani da su ne saboda dalilai guda uku: a samar da Saurin girman dabbobi da tsuntsaye, a kare alamomin murar tsuntsaye a cikin jikinsu da ke sanya ciruta a jiki da yin rigakafin da wata cuta da ke iya kawo masu farmaki nan take.

Magungunan cutar suna da karfin sinadarai da ke yada cutar Bakteriya, amma in cutar ta watsu  magungunan ba su iya yi mata komai, sai an samu na gaba da su waton Antimicrobial Resistance(ARM) saboda cutar ta haifar da kananan cirutocin baktariya da Virus da cima kwance, sinadarin ARM yana kashe su ba tare da bata lokaci ba.

Dakta E. Wesangula AMR jami’i a cibiyar ma’aikatar lafiya ta Kenya a babban taron Afirika da aka kammala kwanan nan a kasar  Nairobi babban birnin Kenya,  ‘Kimiyar manema labarai’ ya fitar da bayani kan hadarin da ya tunkaro kiyon lafiyar mutane a sakamakon watsuwar magungunan  cutar dabbobi.

Matsayarsa ta yi daidai  ga abin da kungiyar likitocin dabbobi ta Nijeriya wadda Farfesa Mohammad Bello Agaie ke shugabanta ta nuna damuwarta ainun kan lamarin na sakakanci da ake yi.  

Dakta Wesangula ya fahimci a yanzu mutane sun fi mayarda hankali ga magungunan cutar dabbobi fiye da na lafiyarsu, masana kiyon lafiya sun nuna damuwarsu kan wannan lamarin. “A kauyukka masu yawa manoma na amfani da magungunan  cutar mutane ga tsuntsaye domin su warkar da su ga wasu cirutoci da suka same su”. Sai ka ga Kaza ba ta da lafiya an jika mata kwayar Farasitimal, ko Kafino da sauransu.

Cin nama da kwai ko Madara da suke dauke da ragin  cutar dabbobi, yana haifarwa mutum sinadaren cutar da ba a gani wadda kwayoyin magani ba su kashewa sai ya yi ta fama a lokacin da ya kwanta rashin lafiya.

Farfesa Bello Agaie ya yi bayanin yanda Magungunan  cutar dabbobi  da ake amfani da su ke zama hadari ga mutane “A duk lokacin da aka sanyawa dabbobi a abincinsu suka ci to a kyale dabbobin har zuwa wani lokaci kar a yanka su in ba a yi haka ba, za a samu ragowar kwayoyin cutar a cikin madara ko namansu.

“Ka ga in ka ci nama, kwai ko ka sha madara ina fada maka ka ci wadan nan cutar a fakaice”.

Farfesa Agaie ya ce abin da yake a zahiri “Abin yafi muni a kiyon kajin gona. Ba ruwan mutane da kiyaye ka’idojin magani suna iya hada kwaya biyu, uku ko hudu wuri daya a ruwa, ba ruwansu da tsuntsayen suna da ciwo ko lafiyarsu kalau, damuwarsu dai girmansu, ko su girma da cuta su dai ba su damu ba.

“Abin da ke faruwa kenan a tsakanin kaji masu yin kwai da masu girman nama mutane na cin kwayoyin cuta a fakaice da sun tafi asibiti don wata rashin lafiya a yi ta baka magani baka samun sauki don kana dauke da kwayoyin cutar da ke kashe maganin da ake baka, saboda kananan kwayoyin cutar sun san yanda suke gujewa  maganin da ake baka ba zai shafe su ba.

“In kuma ka ce baka cin nama, kwai ko shan madara sai dai ka rika cin kai da kafafu da bindin shanu kana karawa kasa taki domin shuka ta samu ta girma, wannan ma magani ne mai kwayoyin cuta cikinsa.” ya bayyana.

Ciyawar da ake samar wa dabbobi tana dauke da ragaggun magungunan kwayoyin cuta kuma tana rage kaifin magani abin da ke sanya kwayoyin cuta habaka in an bayar da maganin kwayoyin cuta ya kasa kawar da ita.

A cewar Dakta Wesangula kusan mutane miliyan 4.2 a Afrika ne ake sa ran suna iya rasa rayukkansu matukar ba a samu maganin da zai kawar kwayoyin cutar dabbobi ba.

Bankin Duniya ma a tashhi kididdiga ta Duniya kan sha’anin lafiya za a lakume kudi da yawansu zai kai Tiriliyan 32 na dala Amerika zuwa shekarar 2050.

Zuwa 2050 Kuma yace kiyon dabbbi da yake kasa a matakin 2.6% zai haura zuwa 7.5% a kowace shekara.

A yanzu duniya ta hau turba na yakar matsanancin talauci (mutum ya rika yini ya malllaki dala Amerika 1.90) zuwa shekarar 2030 da kudirin fitar da kashi uku na mutanen duniya cikin talauci, da Samar da maganin kwayoyin cutar dabbobi yana. Bankin Duniya a shekarar 2016 yace haka. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *