A daren jiya Asabar, 17 ga watan Ogusta, 2019, gwamnonin Arewa sun halarci bikin taya tsohon shugaban jam’iyyar (APC) na ƙasa, Cif John Odigie Oyegun murnar cikarsa shekaru 80 da haihuwa a duniya.

Bikin wanda aka gudanar a babban ɗakin taro na ƙasa da ƙasa da ke babban birnin tarayya, Abuja. Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mai Gida Mustapha, shi ne ya wakilci shugaban ƙasa Muhammadu Buhari. Mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbanjo, shi ne ya kasance babban baƙo na musamman.

Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi, kana kuma shugaban ƙungiyar gwamnoni ta ƙasa, shi ne ya kasance shugaban taro.

Sauran gwamnonin da su ka halarta, sun haɗa da: Gwamnan Jihar Kebbi, kana kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar (APC), Alhaji Atiku Bagudu. Da gwamnan Jihar Plateau, Mista Simone Baƙo Lalong, wanda ya ke kuma shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewa. Sauran sun haɗa da: gwamnan jihar Jigawa da na Kaduna gami kuma da sabbin Ministoci masu jiran rantsuwar kama aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *