Spread the love

                                             BURABUSKON GERO   

Aisha Bashir Tambuwal

Masu bibiyarmu a sashen girke-girke a wannan mujalar MANAGARCIYA ina muku lale marhabin da sake haduwa da mu. A wannan  na kawo muku yanda ake hada BURABUSKON GERO.

Abin da za a tanadar:-

1: Gero,

2: Man girki,

3: Gishiri,

4: Ruwa.

Da farko mace za ta dauko Geronta ta surfa ko ta ba da a surfo mata shi, sai ta fidda dussa akai inji a yi  barzo, a  tankade shi ta fidda gari, sai ta yi aiki da tsakin, daga nan ta dora ruwa madaidaita a tukunya ta yi madambaci, a dauko tsakin a yayyafa ruwa da dan mai da gishiri a cakude shi sosai ,  ta  zuba a tukunyar da ta yi madambaci. Ki tabbata kin rufe shi sosai yanda zai turara sosai, ki ba shi a kalla minti 30, sai ki sauke ki sake yayyafa ruwa sosai amma kada ki bari tsakin ya jike , sai ki kara zuba mai da gishiri kadan (ka da ki bari gishiri yayi yawa)  ki juya shi sosai ki maida shi kan wuta ki koma turara shi,  (kina iya yanka albasa ki saka idan kina bukatata) ki dan ba shi lokaci da ya dafu za ki ji kamshinsa na tashi idan ki ka taba shi za ki ji yayi taushi, sai ki sauke, ki zuba a foodflask.

Anayin na masara kuma ana na shinkafa kuma yanda ake yin wannan haka ake yin sauran, za ki iya yiwa maigida wannan hadin da mai da yaji ko ki soya mai da tarugu ki saka kayan dandano ko ki yi  da miyar taushe ko miyar ganye .

DAN TSOKACI:-

Iya kalolin girke-girke yana daya daga cikin abubuwan da mata ke jan hankain mazajensu da shi , matukar ki ka iya nau’ukan girke-girke kala kala masu dadi za ki ga mijinki yana kara son ki kuma ba zai dinga cin abincin titi ba, duk inda yake yana mararin ya dawo  gida, ba shi babu zaman majalisa don abinci, dan haka ‘yan uwana ku yi kokari ku dage wajen iya kalolin girke-girke.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *