Spread the love

Matar Gwamnan jihar Kebbi Dakta Zainab Bagudu Shinkafi ta yi kira ga Fulani su rika sanya diyansu mata makaranta domin su samu ilmi a yi alfahari da su a cikin al’umma.

Dakta Zainab ta fadi haka ne a lokacin da kungiyar Fulani Miyatti Allah bangaren mata suka kai ma ta gaisuwar barka da sallah a gidan gwamnatin jihar Kebbi. Ta ya ba ma su yanda suke zaune lafiya da sauran al’umma.

Matan sun ba Dakta Bagudu kyautar madarar shanu da Fura da Nono.

Shugabar matan kungiyar Hajiya Hadiza Muhammad ta ce sun zo ne gidan gwamnati su ga uwarsu su nuna mata farincinkinsu ga abin da ta ke yi wa al’ummar Fulani a jihar Kebbi.

Ta ce matan Fulani suna tare da gwamnati za su cigaba da goyon bayanta a kudurorinta na cigaban jiha da kasa baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *