Spread the love

WANNAN HALI NAMU NA YAN NIGERIA……

Daga Rabiu Biyora

Duk da kasancewarta shugabar Maaikatan Gwamnatin Tarayya dake Nigeria wato (Head Of The Civil Service) wacce ke da alhakin dora maaikata akan kyakkyawar hanyar tafiyar da aiki kan ka’ida, har take da ikon ladabtar da wanda yayi kuskure a wajen aiki….

Amma sai gashi wai ita ake zargi akan wasu kudade da suka haura Naira Biliyan Uku, hatta wani yaronta dake temakamata an samu har Naira Miliyan Dari shida a account dinsa, kuma ya kasa bayanin yadda ya samu kudin….

Ni na kasa gane irin wannan lamari namu, da an binciki wane sai kawai kajishi dumu dumu a cikin dukiyar al’umma….

Yanzu haka dai ita shugabar maaikatan tana asibiti a kwance, bayan Tuhumar da tasha a hannun EFCC, baa gama ba an dai dan bata damar ganin likita anan Nigeria karkashin kulawar maaikatan EFCC…..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *