Matan Aure a Borno sun tsunduma a koyon Girki gudun Saki ga mazajensu

Mafiyawan aure yana mutuwa ne a jihar Borno, don kawai matan da aka aura ba su iya girka abinci mai dadi ba.

Maza suna sakin mata ne ta dalilin ba su iya girka abinci mai dadi ba a gidansa, sai ya ga ba hujjar cigaba da zama da matar da ba ta iya abinci ba, sai ya ba ta jan kati ta yi waje.

Hajiya Aisha Musa ‘yar asalin jihar Borno ce da ta fitar da wannan kididdigar a fahimtarta.

Ta ce kan haka ne ya sa ta kirkiro wurin koyar da mata iya abinci mai dadi da lagwada, wanda ta sanya wa suna Na’ish Kitchen, a tunaninta hakan zai sanya aure ya bar mutuwa a jihar ta su.

Wurin koyon abincin ta kirkiro shi watan Junairu 2019 ta koyar da mata 100 zuwa yanzu, kuma mafi yawansu matan aure ne. Yanzu tana shirin fara koyar da 20.

A wajen wurinta kuwa ta koyar da Zawarawa 200 wanda kungiyoyin sa kai suka dauki nauyin horon.

“Ban da wata manufa na fito da wannan sai kawai na ba da tawa gudunmuwa a jiha ta na ganin aure ya daina mutuwa hakan ya sanya mahaifina ya bani goyon baya da karfafani tare da yi min addu’ar samun lada a wajen Allah” a cewarta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *