Spread the love

Alkaline kotun majistare ta Ogudu a jihar Legas ya ki aminta da bayar da belin Dan kasuwa Obinna Amaefula da ake zargi ya yaudari budurwarsa miliyan 4 da dubu 500 ya kuma zubar mata da ciki Dan wata biyar.

Alkali Ejiro Kubeinje ya tsare Obinna gidan yari, duk da bai yarda da laifin tuhuma guda uku da ake yi masa ba, na mallakar kudi da karya, sata, zamba cikin aminci da zagi.

A tabakin mai gabatar da kara Dan sanda Lucky Ihiehie ya ce Wanda ake zargi ya yi yaudarar ne a 20 ga Mayun wannan shekara a rukunin gidajen Atunrase dake Gbagada a Lagas.

Wanda ake zargi ya karbi 4,550 wurin budurwarsa Ese Odobo, da ta kawo kararsa. Da nufin zai saya mata taba jikin motoci guda uku ta cigaba da kasuwancinta da su, daga baya ta gane karya ce ya yi mata.

“Ya yaudareta kullum karya yake yi mata da ba ta uzurin abin da ya sa bai kawo motocin ba.

“Mai koken da ta fahimci yana wasa da hankalinta ne ta nemi ya mayar mata da kudinta, amma sai ya buge da zagi da mare mare duk da yasan tana da ciki.

“Wanda ake tuhumar bayan kwanaki da zagin mai koke ya yi nasarar ba ta kwayar da ta yi sanadin zubewar cikinta Dan wata biyar.” Kamar yanda mai gabatar da kara ya sheda ma Kotu.

Ya ce laifin ya sabawa doka a sashe na 171, 236, 287 da 314 na dokokin manyan laifuka na jihar Legas, 2015.

Majistare ta daga zaman sai 28 ga Augusta don fara sauraren karar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *