Daga Datti Assalafy

Gbenga Adebowale rikakken mai safarar bindigogi da harsashi yana sayarwa masu garkuwa da mutane, rundinar IGP-IRT karkashin jagorancin DCP Abba Kyari sun samu nasaran kamashi kwanakin baya, wanda har yanzu yana tsare ana gudanar da bincike.

Gbenga Adebowale ya yiwa rundinar ‘yan sanda bayani akan farkon haduwarsa da Alhaji Hamisu Bala Wadume gawurtaccen mai garkuwa da mutane wanda yayi sanadin da wasu gurbatattun sojoji suka hallaka dakarun ‘yan sanda bayan sun kamashi, sojojin suka kubutar da shi.

Alhaji Hamisu Wadume ya fara ta’addancin garkuwa da mutane da bindigogi guda 6 da harsashi guda dubu uku (3,000) wanda ya saya a hannun Gbenga, Gbenga ‘dan shekara 35 yace ya hadu da Hamisu ne a dalilin wani yaronsa mai suna Moses a garin Onitcha, shi kuma Moses yana da abokai guda biyu sunansu Dooshima da Delili ‘yan kabilar Tiv ne daga jihar Benue, shi kuma Hamisu abokin Dooshima ne da Delili, suna zuwa su ga Moses wanda suke harkan sayar da makamai dashi, ta yanda Gbenga ya hadu da Hamisu kenan, shekaru 4 da suka gabata.

Sojan da ya bada umarni aka hallaka kwararrun ‘yan sandan mai mukamin Kyaftin bincike ya nuna an tattara kiran waya da yayi tsakaninsa da Hamisu har sau 191, mutuminsa ne da akayi zargin yana bashi kaso na kudi, kuma ya saya mishi mota.

Bayan haka, daya daga cikin kwararrun ‘yan sandan da sojoji suka hallaka, akwai Inspector Mark Philip Ediale ya taba samun yabo daga shugaban sojojin Nigeria a watan 6 na shekarar 2016 lokacin da akayi garkuwa da wani babban hamshakin soji Kanar Sama’ila Inusa aka kashe shi.

Inspector Philip Ediale yana daga cikin dakarun IGP-IRT da aka tura jihar Kaduna domin su farauci wadanda sukayi garkuwa da sojan, sun shafe watanni 3 suna farautan wadanda sukayi garkuwa da sojan, wanda daga karshe suka samu nasaran kama mutum 4 da suke da alhakkin yin garkuwa.

Idan ba’a manta ba Kanar Sama’ila Inusa shine shugaban malamai (Instructor) masu horar da sojojin kundubala wadanda ake basu horo na musamman akan yakin sunkuru, wato Infantry, a shekarar 2016 watarana ya fito a cikin motarsa zai je wani guri sai akayi garkuwa dashi, bayan kwana 2 sai aka tsinci gawarsa, watanni 3 kwararrun ‘yan sandan IRT suka kwashe kafin suka samu nasaran kama wadanda sukayi garkuwa da hamshakin Sojan.

A lokacin ne shugaban sojojin Nigeria Laftanar Janar Tukur Buratai ya sa aka rubuta takarda ta hannun tsohon kakakin rundinar, Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka (rtd) suka aika wa tsohon shugaban rundinar ‘yan sandan Nigeria IGP Ibrahim K. Idris (rtd) suka gode mishi tare da yin jinjina ga kwararrun ‘yan sandan bisa kama wadanda suka kashe musu hafshin soja marigayi Kanar Sama’ila Inusa, cikin kwararrun ‘yan sandan har da Inspector Philip Ediale wanda sojoji suka kashe a Taraba.

‘Yan uwan Inspector Philip Ediale sunyi kira ga Maigirma shugaban Kasarmu Nigeria da ya kawo musu dauki, ya kafa wani kwamitin bincike na masana tsaro wanda babu soja da ‘yan sanda a ciki, suyi bincike akan kisan gilla da aka yiwa ‘dan uwansa a bakin aiki sannan a biya diyya, sunyi korafin cewa sojoji sukayi laifi na kisan ‘dan uwansu, bai kamata sojoji su jagoranci binciken ba, tunda a karon farko ma sun fitar da sanarwa suna kokarin bada kariya ga sojojin da suka aikata laifin kisan gillar.
Mai neman karin bayani ya duba jaridar Vanguard na shekaran jiya da kuma na jiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *