Spread the love

Mahara da ake zargi masu garkuwa da mutane ne sun sace matar aure dauke da juna biyu a kauyen Katura na karamar hukumar Dange Shuni a sanyin safiyar Alhamis din nan.

Majiyar da ta yi wa manema labarai bayani ta ce sunan matar Luba an dauke ta da misalin biyun daren Laraba a gidan mijinta dake zango 15 tsakaninsa da Sokoto.

Majiyar ta ce maharan sun kai su 7 sun shiga Katura da harbin mai kan uwa da wabi don tarwatse jama’a, sun yi wa mijinta Dan banzar duka kafin su tafi da matar.

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda Sadiq Abubakar ya tabbatar da jami’ansu na Dange Shuni sun samu kiran waya mahara bakwai sun shiga Katura sun dauke mai ciki da ake kira Halima wadda aka fi sani da Luba Bello.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *