Spread the love

Sabon rikici ya kunno a masana’antar shirya finafinnan Hausa. Jarumi Mawaki Adam A Zango ya fita kungiyar shirya finafinnan Hausa daga yau 15 ga watan Augustan 2019.

Jarumin ya bayyana wannan matakin ne a turakarsa ta Instagram. Ya ce duk wani mai son Hulda da shi ta aiki ya tuntubesa ba tare da jin shi Dan kungiyar ne ba, abtsarin doka ba in da aka ce dole sai ya zama Dan kungiya amma duk Wanda zai mu’amala sa shi ta zama wajen kano ne in dai ta aikin sa ce.

Zango ya dauki wannan mataki ne bayan yi wa darakta Sanusi Oscar 442 walakanci da kulle shi gidan yari, in da shi ma jarumi Mustafa Naburaska ya ce ya bar wasan Hausa sai bayan mulkin Ganduje zai dawo.

Wannan sabon rikici ne ya kunno kai a masana’antar shirya finafinnai ta Hausa Wanda ba a San in da lamarin zai tsaya ba ganin wata mata ba ‘yar film ba ce ta zargi Ali Nuhu da yin munafunci a wurin kama daraktan don kawai suna da bambancin siyasa.

Siyasa da alama ita ce za ta tarwatse masana’antar shirya fim na Hausa matukar ba a yi wa tubkar hanci ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *