Spread the love

Sanata Shehu Sani y ace rashin adalci ne Arewa ta qi miqa mulki a 2023.

Sanatan wanda wanda ya waqilci Kaduna ta tsakiya a majalisa ta takwas ya ce abu ne da ba za a yarda da shi ba Arewa ta cigaba da mulki bayan shugaba Buhari ya kammala wa’adinsa a 2023.

Ya yi wannan kalamai ne a gidan tsohon gwamnan tsohuwar Kaduna Balarabe Musa a lokacin da ya kai masa gaisuwar barka da Sallah.

Ya ce Buhari ya samu nasara ne na darewa kan kujera a 2015 saboda goyon baya da ya samu ga wasu bangarorin qasar nan bayan shan kaye har sau uku da ya yi.

Sani ya qara da cewar abin da nake gani anan sauqi gare shi, kawai duk dan Arewa ya jingine maganar 2023 domin ta ‘yan kudu ce musamman kudu maso yamma domin sun ba da matuqar gudunmuwa dan Arewa ya zama shugaban qasa a 2015.

Ya ce Yakamata Areawa su gode da goyon bayan da suka samu ga kudu ta yamma ko Kudancin gaba daya suka aminta aka canja PDP a 2015.

Arewa ta gyara gidanta ta magance matsalolin da ke addabarta na qabilanci da yanki domin samun cigaba. A cewarsa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *