Spread the love

Jami’a Mallakar jihar Sokoto za ta fito da sabbin tsangayoyi guda uku

A wannan shekarar da muke ciki Jami’a mallakar jihar Sokoto za ta soma gudanar da wasu sabbin tsangayoyi guda uku.

Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya sanar da hakan a lokacin da ya karbi shugaban jami’a Usman Danfodiyo Farfesa Sulaiman Lawal Bilbis da Shugaban jami’ar Sokoto Farfesa Sani Muhammad Dangwaggo  da suka  kawo mashi gaisuwar barka da sallah a fadar gwamnatin jiha.

Tambuwal ya yi bayanin tsangayoyin da za a kirkiro da suka hada da tsangayar magani(Medicine) da tsangayar  sanin kimiyar zamani(ICT) da tsangayar kimiyar Muhalli(Environmental Technology).

Ya ce yanke shawarar fitowa da tsangayoyin domin a tabbatar da asibitin koyarwa ta jami’a mallakar jiha ta tafi da aiyukkanta yanda yakamata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *