Spread the love

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci bankin kasa da ya daina baiwa masu fataucin abinci kudaden kasashen waje don shigo da abinci Nijeriya.

Buhari ya fadi haka a garin Daura ta jihar Katsina a lokacin da ya saukar da gwamnonin APC abincin sallah babba na rana.

A cewarsa umarnin zai daidaita yanayin harkar noma da tsaron abinci.

Bayanin Wanda babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa Buhari, Malam Garba Shehu ya yanko kalmomin Buhari yana cewa kudaden za a iya amfani da su wajen kara habaka tattalin arziki, kuma za a daina dogara da abincin kasashen waje.

“Kar Ku ba su ko senti daya don su dauko abinci kasashen waje” a cewar Buhari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *