Maɗigo da Luwadi ne suka Jefa Najeriya cikin matsalar rashin tsaro ––Sarkin Gwandu

Maɗigo da Luwadi ne suka Jefa Najeriya cikin matsalar rashin tsaro ––Sarkin Gwandu

Sarkin Gwandu kuma shugaban sarakunan jihar Kebbi, Mohammadu Iliyasu Bashar ya bayyana cewa yawaitar aikata ayyukan ashsha da mutane ke yi yanzu ne ya jefa Najeriya cikin halin da muke ciki na rashin tsaro.

Sarkin Gwandu ya fadi hakane da yake jawabi a filin Idi bayan kammala Sallah.

“Aikata ayyukan alfasha da suka haɗa da madigo da mata ke yi yanzu da luwaɗi da maza ke yi su ne suka sa muke ta fama da matsaloli dabam-dabam a ƙasarnan.

Sarki Gwandu ya ƙara da cewa idan ba dawowa ga Allah jama’a suka yi ba, za a ci gaba da faɗawa cikin matsaloli na tashin hankali, kashe-kashe da rashin zaman lafiya a ƙasarnan.

Sannan kuma ya yi kira ga mutane da su ci gaba da yi wa ƙasarnan addu’a domin samun zaman lafiya da ci gaba.

A jawabin sa, Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Bagudu ya jinjinawa shugaba Muhammadu Buhari kan saka hannu a kudirin maida kwalejin koyon ayyukan gona ta Zuru zuwa Jami’a.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *