Spread the love

Shugaban kasa Muhammadu buhari ya ajiye Ita Enang amatsayin mai ba shi shwara kan harkokin majalisar dattijai.

Mista Ita Enang tsohon sanata ne daga jihar Akwa Ibom an nada sh mai baiwa shugaba Buhari shawara a wa’adin mulki na farko.

Ya cigaba da zama mai rikon kwarya a wa’adi na biyu kamar sauran wadan da Buhari bai sabunta wa’adinsu shi ma ya ajiye shi.

Wata majiya ta kusa ga fadar shugaban kasa ta gayawa jaridar Premium a lahadi da marece Buhari ya ajiye Ita ya dauko Omoworare Babajide tsohon Sanata daga jihar Osun ya maye madadinsa. a cewar majiyar.

Fadar shugaban kasa ba ta yaba aikin Ita ba yadda hulda tsakanin Majalisa ta 8 da shugaban kasa ta gudana duk da shi tsohon sanata ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *