Gwamna Zulum ya biya kudin Hadayar Mahajjatan Borno 1,718

Gwamna Zulum ya biya kudin Hadayar Mahajjatan Borno 1,718
Domin karfafa guiwa ga yin addu’ar zaman lafiya mai daurewa Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya aminta da biyan kudin ragunan Hadaya na kowane Mahajjaci daga cikin 1,718 da suka fito daga jiharsa don su yi wa Borno addu’a a Makka lokacin  Arafa.
Hawan Arafa yana cikin wajiban Hajji duk Wanda bai yi shi ba ba ya da Hajji, addu’a a wurin karbaba ce.
Sakon na gwamna ya kara karfafa mahajjatan Borno ya zo ne Jim kadan bayan saukarsu daga Arafa in da aka hada malamai na manyan yaren Borno Hausa da Kanuri da Shuwa Arab da Babur, babban sakataten jindadi da walwalar Majjata na jihar ya sanar da labarin ga mahajjata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *