Spread the love

Gwamnan Zamfara Bello Matawallen Maradun ya aminta da saukar da Sarkin Maru Alhaji Abubakar Cika da uban kasar Kanoma Alhaji Lawal Ahmad a sanarwar da mataimakin gwamna Barista Mahdi Aliyu Gusau ya fitar kan saukar da Sarkin da Uban kasar.

An dakatar da Sarkin a watan Yuni kan zarginsa da hada baki da mahara da barayin shanu a jihar.

Kwamitin tsohon shugaban ‘yan sanda MD Abubakar da gwamnati ta kafa domin ya binciki matsalar tsaro da hanyoyin magance ta shi ne ya aminta da a cire Sarkin tare da Uban kasar..

Uban kasar yana cikin rikon Masarautar Maru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *