Spread the love

MUHAWARA

Abokantaka waton hulda ta aboki da aboki tana da matukar muhimmanci a rayuwa ginshiki ce ta tafiyar lamurran rayuwa su yi kyau da inganci, anan muna son mu duba halin da yakamata mutum ya aikata bayan da abokinsa ya ci amanarsa.

Cin amana yana nufin mutum ya sabawa gaskiyarka da shi ya aikata wani hali wanda ba ka yi tsammani ba, wanda zai sosu a ranka sosai in da za ka samu kunar zuciya, da ba shi ya aikata halin ba ko kadan ran ka ba zai damu ba.

Dole ne a samu mabambanta ra’ayi kan mi yakamata ka yi idan abokinka ko dan uwanka ya ci amanarka.

“Idan na samu cin amana daga wurin wadan nan mutane zan yi shiru abina ba zan sanar da kowa ba kuma ba zan yake hulda ta da su ba, sai dai zan kiyaye gaba ba zan bari hakan ta sake faruwa ba.” a cewar Sadiya Attahiru Jabo

Ta kara da cewar “Cin amana yana taba zuciya sosai musamman idan abokinka ko dan uwanka ya yi maka, yarda da su kawai ta kare zan canjawa abokina matsayi a zuciyata, zan nemi wani kawai shi na aji ye shi.” in ji Sadiya.

Muhammad Muhammad ya ce “Zan tuno duk wata alaka tsakanimu in yanke ta gaba daya, in goge hotunansa da duk wani sakonsa da ke hannuna. Ni ina matukar kaffa-Kaffa a wurin zabar aboki, ba yanayin da zai sanya na kira wanda ya ci amanata abokina” in ji Shi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *