Spread the love


“A wannan shekarar da muke ciki ba a samu wani bambanci  sosai ba a farashin Raguna yanda mutane suka sani ne, Ragon da ke Layya anan wajenmu farashinsa daga  dubu 30 ne zuwa sama har 100 da kari akwai”

Shugaban Kungiyar masu sayar da Raguna da Awaki na Sakkwato Alhaji Isa Bello Unno Sabon Birni ne ya furta hakan a zantawarsa da manema labarai kan yanayin kasuwar dabbobi a wannan shekara. Ya ce kasuwa ta Raguna sai dai su yi wa Allah godiya kamar yadda aka saba duk shekara irin wannan lokaci za a sami Raguna masaya ma za su shigo kasuwa domin saye.

Isa ya ci gaba da cewa “Ba mu fatan farashi ya daga duk da alamu sun nuna hakan domin kullum sai an dauki Raguna 200 cikin kasuwar nan ta mu ta Kara zuwa kasar Nijar, dabbobinmu sun fi nasu mai; farashin yana iya haurawa in Ragunan suka rage yawa a wajen masu sayarwa.”

“Amma wannan ba tabbas duk da a wannan shekarar ma abincin dabbobi ya yi sauki da rahusa, in aka samu abincin dabbobi ya samu ba tsada a wurin sayensa tau dabbobi kara farashi suke yi, saboda ba kowane mai kiyo ke sayar da dabbarsa ba a lokacin da abincinta ke da sauki, mafiyawan mutane suna sayar da dabbobinsu in abinci nada tsada domin kiyo a lokacin yana da wahala, a shekarar data gabata kwalfar wake buhunta ya kai 5000 yanzu tana kasa da 2400 ba kowa ke sayar da dabbar shi ba, wannan yana kawo tashin farashin dabbobi ko ba a lokacin layya ba” in ji shi.

Alhaji Bello ya duba yanayin masaya ya ce shekara uku da suka gabata kasuwancin ya canja ba kamar shekarun baya ba da suke fara hada-hadarsu tun Salla saura kwana 30 ba amma yanzu sati daya ne suke ciniki sosai, yayi kira ga masu sayarwar dabbobi a ko’ina suke da su sassautawa masaya domin ibada ce za a yi.

“Da zaran gwamnatin Sakkwato ta shigo ta sayi Ragunanta 500 da ta ke saye gare mu cinikinmu zai motsa kuma sai ka ga abubuwa sun sauya gwargwado domin mutanen kasuwa za su amfana.” Ya ce.

Ya yi godiya ga gwamnatin Sakkwato kan filayen da aka ba su suka gina shaguna a kasuwar, ya kuma musanta zargin da ake yi na gwamnati ta karbe filayen ne ga wasu ta baiwa Kungiyar.

“Duk wanda ke wannan maganar harka ce ta son rai fili na gwamnati ne aka rika zuba shara wurin muka nemi Gwamna Tambuwal ya ba mu ya aminta aka rabawa mutanen kungiyarmu suka gina shaguna ana kasuwanci. Bayan karamar asibitin dabbobi da aka yi mana akalla muna tare da likita biyar anan da yake duba mana dabbarmu duk mai wata cuta ana fitar da ita ta sha magani.” In ji Isa.

Yusuf Hussain jami’in hulda da jama’a na Kungiyar masu sayar da shanu ta jiha ya ce “Duk wani mai son yin layya da Maraki sai ya samu na dubu 250 har zuwa sama, in ko karin nama yake so kawai a layyarsa ta Rago da ya yi, ana sayen na dubu 50 ko 80 ko 120 ya danganta da halin mutum.  A wannan shekara an fi sayen Shanun layya fiye da bara akwai mutum daya da ya zo ya sayi Maraki 20 a kasuwar nan ta Kara kuma layya za a yi da su, kuma a wannan shekarar an fi samun masu mai duk an san a lokacin damina shanu ba su Mai, hakan baya wuce nasaba da yanda ba a kawo mana shanun daji ba, kusan dukkansu na gida ne kiyon gida suka samu.” kalaman Yusuf

Ya kara da cewar yanda gwamnati ke kula da lafiyar dabbobinsu abin yabawa ne bayan zuwa da take yi tana sayen shanun layya a wurinsu. 

A mafi yawan wuraren da ake sayar da raguna a Sakkwato za ka samu akwai karancin masaya sosai, kuma dabbobin suna da tsada ba kasa Ragon dubu 30, amma ana samun Tunkiya ta 28 mai girma haka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *