Akan haka ne yakamata mutane su rika tafiye tafiya da hankali domin tsira daga fadawa cikin wadansu matsalolin hadari da zai sanya a samu rauni ko salwantar rayuwa.

  Hadari da ya auku cikin dare farkon Shiga Garin Aliero dake jihar kebbi wanda ya rutsa da mutane 4 da suka rasa rayukkasu yayin da wadansu kuma suke kwance Asibitin suna jinyadaya motar kirar kanta ta fito ne daga Kudancin Najeriya dauke da  lodin Goro, yayin da ta yi taho mugama da dayan kantar ana zargin Barci ne ya rinjayi dayan direban da yake dauke da lodin Goro abinda ya sa Motar ta kwace masa ta tarbi dayan mota Wanda yakai ga rasa rayukkan mutun 2 daga cikin kowace motar.

A daidai lokaci da  Sallar laiya(Babbar Salla) ke karatowa   hidimomi da uzurikka da tafiye tafiye da cinkoson ababen hawa na karasowa 
Saboda haka matsaloli na faruwa a tsakanin alumma da ke tafiye-tafiye daga yankunan da suke zaune domin dawowa gida hidimar Sallah

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *