Spread the love

Gwamna Zulum ya biya kudin jarabawar kammala Sikandaren dalibai 24,323 na jahar Borno

Daga Alaji Engr Ibrahim Ismail,

Mai Girma Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya amince da sakin naira million dari da hamsin da biyu da digo shida (152.6M) a biya kudin jarabawar kammala Sikandaren dalibai dubu 24,323 na jahar Borno da suka rubuta jarabawar WAEC na bana May/June 2019

Mai magana da yawun Gwamnan Malam Isa Gusau shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa daya fitar a yau Juma’a, a cewar sa, kamar yanda Gwamnatin jahar Borno ta saba na biyan kaso 45%, karamar hukuma kuma kaso 30%, da kuma iyayen yara su biya kaso 25% cikin dari na kudin jarabawar.

Gusau ya ce amincewa da biyan kudin ya biyo biyan izini da sakataren dindin na Ma’aikatar ilimi na jahar Mohammed Mustapha Abacha ya nema.

Gwamnan yayi fatan daliban jahar za su samu kyakkyawan sakamako a jarabawar da suka rubuta a bana.

Zulum yayi kira ga Iyayen yara da malaman makaranta su jajirce wurin baiwa dalibai inagantaccen ilimi a jahar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *