Wannan Asibiti dake kauyen Sabiyel cikin Karamar hukumar mulki ta Aliero  
An ginata ne tun tsakanin Shekarar 2003 aikine na Dan Majalisar Dattawa na lokacin wanda ya wakilci Kebbi ta tsakkiya 
Amma tun bayan gina Asibitin da akayi da kayan aiki da aka saka mata ba’a taba budeta da niyar yin aiki cikinta ba 
Domin a ziyarar dana kai garin na Sabiyel na samu babu kowa a cikin Asibitin sai kadangarai da kusa  da sauran kwari 
Amma Kuma alamu yanuna akwai Wanda ke gadi a cikin asibiti inda naga ayi shukar gyada a cikin ta har zuwa kofar shiga cikinta 
Amma yanayin da Asibitin take ciki na mugun hali yasa tana bukatar kulawar gaggawadomin saman  rufinta yafara tashi yayin da ruwan sama suke shiga cikinta a duk lokacin da anka samu ruwan sama

A saboda haka yakamata hukomomin da abin ya shafa daga Karamar hukumar mulki ta Aliero har zuwa Ma’aikatar lafiya ta jihar kebbi dasu kaiwa wannan Asibiti daukin gaggawa domin idan aka duba anginata ne domin tallakkawa gashi kuma tanada girman da za’a iya kulawa da jinyar mutanen kauyukkan dake kusa da garin Sabiyel

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *