Gwamnatin jihar Sakkwato, Ta Raba Naira Miliyan 17 don yi wa Marayu da tsoffi maras galihu Layya.

Gwamnatin jihar Sakkwato, karkashin jagorancin Aminu Waziri Tambuwal Ta raba naira Miliyan 17, da 200,000:00 don yi wa Marayu da Tsoffi Marasa Galihu Layya.
 Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya kaddamar da rabon kudaden layya ga uwayen kasar   gundumomi 86 dake fadin jihar Sokoto.
Sarkin Musulmi,ya yabawa Gwamnatin jihar na daurewa da wannan shirin. 
Sarkin Musulmi ya kuma jinjinawa Hukumar Zakka da wakafi ta jihar Sokoto, akan kokarinta na dagewa da wannan aikin, kuma ya yi kira ga Sarakunan da aka baiwa wannan amanar da su sani duk wanda ya ci hakkin maraya to yaci wuta, kuma  majalisar ba za ta lamunce ba.

“Kar wani uban Kasa ya sanya siyasa a cikin aikin duk mai wata jam’iya a jiye ta gefe ya yi aiki saboda Allah ba tare da nuna bambancin siyasa ba, ku sarakuna ne duk wani mai mulki na siyasa da zo zai yi aiki da ku don ku na kowa ne don haka a wannan aikin ka da wani ya sanya siyasa a ciki aiki ne na Allah a yi saboda shi” a cewar Sarkin Musulmi  
Tun farko, Shugaban Hukumar Malam Muhammad Lawal Maidoki, Sadaukin Sakwwato ya ce gwamnan jihar Sokoto ta aminta da kashe kudi Naira miliyan Goma Sha Bakwai da dubu Dari biyu , domin sayen shanu na layya ga marayun da ba su da hali dake  fadin gundumomi 86 a kananan hukumomin jihar 23. 
Maidoki ya ce kudin za su kasance kowace gunduma za ta karbi Naira dubu 150, domin sayen maraki, naira dubu 10 na aikin gyaran naman da wasu naira dubu 10 domin zirga-zirga ga ‘yan kwamitin, kowace gunduma za ta amshi naira dubu dari da Saba’in (170,000:00).
Sadaukin Sakkwato,Ya kuma yabawa gwamnatin jihar akan wannan kokarin yau shekar biyar ana yin sa, ya kuma yabawa majalisar Sarkin musulmi akan goyon baya da shawarwarin da ta ke baiwa Hukumar, ya kuma sanar ba iyayen kasar da ka da su sanya siyasa a cikin wannan Lamarin, Ya sanar cewa za su nada kananin Kwamitocin da za su zagaya domin ganin yadda aka yi da wannan amanar ta hakkin marayun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *