Spread the love

Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta samu nasarar cabke wasu mutum biyu da ake zargin sun yi wa wasu kananan yara mata fyade a jihar Sokoto.

Kwamishinan ‘yan sandan Sokoto Ibrahim Ka’oje a lokacin da yake gabatar da masu laifin ga manema labarai ya ce ” Ranar 27 ga watan Juli ne aka kama Bello Umar a kauyen Dogon daji cikin karamar hukumar Tambuwal da zargin ya yi wa Zainabu Abubakar ‘yar shekara 11 fyade a gidansa dake garin, wanda ba da sonta ba hakan ya faru. Muna kan bincike da zaran an kammala za mu kai shi kotu” a cewar Ka’oje.

Haka ma ya ce sun samu nasarar kama Khalifa Sani a kuyen Kunbula a karamar hukumar Sabon Birni ya yi wa wata Fatima Hassan mai shekarru 15 fyade a cikin daji, a lokacin bincike mai laifin ya karba laifinsa.

Bayan kare wannan bayani manema labarai sun tattauna da masu laifin in da Bello ya musanta laifinsa ya ce shi bai aikata abin da ake zarginsa ba. Amma Khalifa ya aminta da ya aikata laifin da ake zarginsa sai dai ya yi hakan ne da yardar wadda ya yi wa “ta tona asirin ne domin ta ji tsoron wadan da suka zo wurin kar su kama mu, na ba ta 400 da yarjejeniyar bayan mun kare zan ba ta Kankana ta je da ita gida mun shirya tun a gida domin tana zuwa gidanmu” kamar yadda ya furta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *