Spread the love

                   

Managarciya: A matsayinki na dadaddiyar mawakiyar Hausa wadda mutane suka kwashe shekaru sama da 15 suna jin muryarta a fina-finan Hausa, wadanne abubuwa ne ki ke ganin suna yi maku tarnaki wajen ci gaban ku.

Murja:  Da farko dai suna na Murjanatu Yakubu Baba, wadda aka fi sani da Murja Baba ko ‘Yar Baba. To gaskiya abu daya ne tak ke yi mana tarnaki a wurin ci gaban mu, wanda har yanzu mun kasa magance shi, hadin kai babu shi a cikin harkarmu, duk abin da baya da shugabanci akwai matsala, kuma ba za a taba hada kai ba, wannan shi ne ke jawo mana duk matsalolin da ke addabarmu a cikin masana’antar wakokin Hausa na fim.

   Takwarorinmu na sauran kasashe muna da tsari iri daya da su, amma duk sun fi mu ci gaba don kawai bamu da hadin kai ga kuma hadama. Za ka ga mutum daya shi ke kida da waka da miksin ba wani mai ba shi umarni, ba wai na ce wannan ba kwarrewa ba ne, sai dai abin nan ya hana mana karko don mawakan kasashen waje za ka ga akwai mai shiryawa daban, da mai rubutawa daban, da mai gyara murya da mai kida duk daban. To amma mu bama yin hakan, mutum daya zai hade wadan nan duk shi kadai, ka  ga babu batun inganci a nan, da mun yi abu lokaci kadan sai ka ga ya bace don babu jagoranci ana ganin wannan wayewa ce. Wallahi wannnan shirme ne abun da muke yi na kwakwalwa ne, yana bukatar  taimako da tsari da hankali, ba komai a ce kai kadai za ka yi ba.

Managarciya: Bari na mayar da ke baya, me ya baki sha’awa ki ka shigo harkar wakokin fim na Hausa.

Murja: Haka ne, gaskiya  ni tun da na taso ina sha’awar wakoki, tun ban san mene ne burgewa ba, na tsinci kaina mai yawan son rera wakoki har a makarantar Islamiyar da nake karatu, ni ce ake baiwa kasidu ina rerawa a lokacin maulud da kuma makarantar kwana da na yi, in za a ba da hutu mukan yi waka. Haka ne na tashi da waka har zuwa yau, na yi wakoki da ban san adadinsu ba, don duk wanda ya ce na jero su, ya hadani da aiki, tun daga shekarar 2000 in na dauko zuwa yanzu shekara 19, kuma ba a lokacin na fara waka ba. Na yi wakar ‘fifita mana shayi’  da ‘Zarafin kauna’ da wakokin ‘Daham’ tare da Yakubu Muhammad da ‘Kwalli ya sa ido shanawa’ da ‘Jarumai sun karya alkibla’ ga sunan da yawa ba zan iya kirga su ba, don a lokacin duk wakar da ka ji Yakubu Muhammad ya yi to tare da ni ce, irinsu ‘Gara aka mini gara ake shirin aure wayyo mijina dawo kabar batun gara’ da sauransu. Haka mawaki Adamu da Abubakar Sani ‘Bakin ganga’  ‘Sakalim baye ayyara iyye salim baye”. Sani Danja ma wakokin “babbar riga” da ‘gurgu mai dala’. In ka dawo wurin sababbin mawaka irinsu Umar M. Sharif  a wakar shi ta Hallacci ‘ka daure ka yi min hallacci’ da Adamu Nagudu wakokin ‘sirri’ na kwanan nan, da Hussaini Danko wanda kusan yanzu na fi waka da shi don duk su ‘tafiya da gwaninka akwai dadi’ da ‘basajarmu a so saura kiris’ da ‘ga dodon maza’ da “so aljanar duniya’ duk dai ga su nan, ba adadi, in takaita maka duk mawakan da, dana yanzu ba wanda bana waka da shi.

Managarciya: Akalla kin fi shekara 19 kina wakoki wadanne irin kalubale ne ki ke fuskanta a harkar sana’arki.

 Managarciya: A duk wakokin ki ko akwai wadda tafi baki wahala ko take burge ki  sosai?

Murja: Ni Murja Baba bana wakokin batsa kuma  ba wata waka da ke bani wahala, sai dai idan mutum ya soma fara waka takan yi masa tarnaki kadan. Wakar “Zarafin kauna” da muka yi da Adamu Nagudu ta bani wahala sosai, na yi  awa hudu a wurin rera ta, na kasa gane rashin sabo ne ko wakar ce mai wahala, domin akwai wakoki masu wahala. Wakar da na fi so take burge ni ita ce ‘Na rike manzon Allah na so Annabi mai kyauta, zuciya ta kullum kwadayinta Annabi ne shar  shar’ wannan wakar ita ce ta sanya tsohon Kakakin Majalisa na Kano ya biya min aikin hajji.  Sai kuma wakar da na yi wa masoyana, ina kaunar wakar da alfahari da ita domin masoyana su ne ni, da za su sanya a yi alfahari da ni, ‘jinjina masoyana, Murja Baba ina murna, gaisuwa cikin murna domin kuna muradina, addu’a ku ke guna, Allah sa mini albarka’. 

Managarciya: Kina da alaka ta jini da Maryam A. Baba ?

Murja: Gaskiya ban da wata alaka da Maryam A. Baba ta jini, sai dai ‘yar uwar sana’a ta ce kawai, kuma mun fi mu’amala da ita bisa ga sauran mawaka. Rayuwar waka ce ta hada mu, ita da Zainab A. Baba ne suke uwa da uba daya.

Managarciya: Shawararki ga mawaka 

Murja: Ina kira ga ‘yan uwana mawaka mata, da su kare kansu da mutuncinsu in aiki ya zo mana, mu yi yanda ya kamata, ba cuta ba cutarwa, mu rike amanar junanmu kar mu cutar da kanmu, Allah ya sakawa kowa da alheri, har mawaka maza domin ni ina da kyakkyawar alaka da kowa. Su kuma masoyana na gama ba su sako, don na ce masu alkawali na dauka zan so ku kamar ni kaina, addu’ar da ku ke yimin ina gani, Allah ya saka ma ku da alheri sosai.          

Murja: Kalubale dole ne mutum ya rika fuskantarsa a kowace harka ta nema, amma wadda tafi damuna ita ce kallon da ake yi mana a gari a matsayin ‘yan iska lalatattu, da iyayenmu da aurenmu da komai sana’a muke yi kamar yanda mata masu aikin jinya da ma’ikatan banki, duk da maza suke yinta, sai dai su ba a kiransu da ‘yan iska sai mu, wanda hakan bai dace ba, ni a gaban mahaifana na ke, mijina da uwata da ubana duka suna raye, kuma idan bani da aiki ban fita ko’ina, kuma da na kamala zan dawo, a gaskiya sunan ‘yan iska da ake kiranmu ya na damu na.

       Shahararriya kuma dadadiyar mawakiyar Hausa da sunanta ya zagaye duniyar fina-finan Hausa, wato Murja Baba,ta samu zantawa da mujallar managarciya kan harkokin waka da abin da ke yi masu tarnaki a harkar sana’ar ta su, da sauran batutuwan da suka shafi harkar waka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *