Spread the love

LABARIN  SARKI MAI MATA DAYA DA  ‘YA DAYA.

Kirkiren labari ne

    Akwai  wani sarki  mai mata daya da ‘yarsa daya mai suna Kulu, kwanci tashi ku dai, Allah Ya yi wa matar sarkin nan rasuwa. Bayan dan wani lokaci, sai sarkin nan ya auri wata Bazawara, ita kuma tana da ‘yarta  mai suna Zainabu da ta zo da ita(Agola).

    Bayan amaryar sarki ta tare ne, sai ta sanyawa Kulu karan tsana, a kowace rana sai azabtar da ita ta ke yi.  Wannan mata ta yi ta tunanin yadda za ta gama da Kulu, ta bar ganinta gaba daya amma ta rasa samun haka.

   Daga karshe sai ta ce da ‘yarta, Zainabu watau (agolar Sarki) idan sun je rijiya debo ruwa, ta sanya Kulu diban ruwa. Idan ta zura gugar cikin rijiya, ta fara janyo ruwa, sai ta ingiza ta cikin rijiyar. Haka aka yi kuwa, da suka je sai Zainabu ta baiwa  Kulu abin diban ruwan, sai  ta tsaya a bayanta, Kulu na gama zura guga, kafin ta an kara, ba ta fara jan ruwan ba, Zainabu ta ingiza ta cikin rijiyar, ta kuma kama hanya, ta koma gida abinta. Da ta yi wa mahaifiyarta bayanin ta cika aikin tura kulu cikin rijiya, sai  ta ce kin kyauta, mun huta da ‘yar banza.

    Ashe aikin da ta yi, an kashe Maciji ne ba a sare kansa ba! Rijiyar  da aka tura diyar sarkin nan, ta na kan hanyar da sarki ke bi. A kodayaushe idan zai fita kilisa ko kewayar kasarsa kusa da rijiyar yake wucewa. A wannan ranar  ma ya biyo ta wurin lokacin da yake dawowa daga wani  tattaki a kan dokinsa, makada da mabusa na binsa a baya suna yi masa kirari suna cewa:

Sarki mai duniya,

Sarki  gatan Kulu.

Da Kulu ta ji sai ta ce,

“Uban Kulu, ko Uban Zainabu?

Zainabu taji dadinta,

Ga ubanta ya zo gida,

Amma ga Kulu nan a cikin rijiya”.

Sai wani dogari ya ce. “Ku yi shiru ku ji”.

    Da suka yi tsit, sai suka sake jin wakar, nan  take aka gane lallai muryar Kulu ce. Ba tare da bata lokaci ba aka shiga rijiyar, aka tsamo Kulu. Ta ji jiki sosai, domin ta sha bugun bangon rijiyar nan lokacin da aka ingiza ta ciki. Mamaki da haushi suka kama sarki, amma ya shanye, bai nuna fushinsa a bainar jama’a ba. Tun a bakin rijiyar ya tambaye ta yadda aka yi ta auka cikin rijiya, Sai ta yi masa bayanin yadda agolarsa,watau Zainabu ta ingiza ta.

     Bayan sarki ya koma fadarsa ya huta, sai ya kira amaryarsa, bai ma jira ya ji abin da za ta ce  game da inda Kulu ta ke ba, ya sanar da ita cewa zaman su ya kare.Ya bayar da umarnin a kwashe kayanta gaba daya, ya kara mata da dukiya mai yawa, ya ce a mayar da ita ga mahaifanta.Ya ci gaba da zama da Kulu, Kafin ya sami wata macen kirki ya aura.

Kurunkus.

     Da wannan labari ne za ku fahimci cewa, kar  ku yarda a tura ku; ku yi wa wani sharri, da zaran ku ka yi abin, zai dawo kuma ya shafe ku, har da wanda ya tura ku, daga nan sai ku rika yin dana sani. Don kaucewa dana sani, ku rika biyayya ga aikin alheri.

    Wannan ita ce gudunmuwar da zan ba ku da fatar kun san mugunta ba kyau, idan zaka gina ramen mugunta  ka gina shi  gajere don ba ka sani ba ko kai za ka fada.

Ni ce Ta ku

UMMUL-KHAIR SHEHU AMBURSA.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *