Spread the love

Bayan shekara 20 gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ce za ta sake duba tsarin rabon kudin kasa, za a duba na gwamnatin tarayya da jihohi da kananan hukumomi, kan yanda hakikanin tattalin arziki yake a yanzu.

Shugaban hukumar tattara kudin shiga da raba su Mista Elias Mbam ya bayyana haka ga manema labarai a birnin Abuja jim kadan bayan ya karbi lambar yabo da kungiyar ma’aikatan gwamnati suka ba shi.

Yanda tsarin yake a yanzu gwamnatin tarayya ta na da kaso 52.68, jihohi na da kaso 26.72, kananan hukumomi na da kaso 20.60.

Kaso 13 na Man gas da Fetur yana komawa ga jihohin da suke da arzikin man Fetur domin su kula da yanda man ke samar da zaizayar kasa da wasu hadurra da ke tasowa.

Tsarin an samar da shi lokacin gwamnatin Shugaba Obasanjo, hukumar ta shiga neman bayanai kan yanda za a tafiyar da lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *