EFCC a yankin Sokoto ta kwato Takin zamani da maganin kwari da kudinsu yakai miliyan 17

Hukumar kula da cin hanci da rashawa yankin Sokoto mai kula da Sokoto da Kebbi da Zamfara ta kwato takin zamani da maganin kwari na kimanin miliyan 17 da dubu 100, da Ibrahim Rijiya ya karkatar da hadin bakin mai kula ma’ajiyar kayan Aminu Musa in da suka sayarwa Abdullahi Bashir

Shugaban yankin Abdullahi Lawal ne ya furta hakan ga manema labarai a jihar Sokoto ya ce sun samu bayanin ne a hannun wasu kungiyoyin manoman shinkafa 17 dake garin Gummi karamar hukumar Gummi ta jihar Zamfara sun kawo korafinsu na gwamnatin tarayya ta ba su taki tirela uku da maganin kwari kanta guda amma sun yi sama ko kasa ba a gansu ba.

Ya ce sun yi bincike suka gano kayan kuma sun kwato su har sun rabewa manoman kayansu saboda lokaci ne na damana ba za su bar kayan a hannunsu ba tun da ana bukatarsu a yanzu.

“Mun bayar da wadan da ake tuhuma beli domin kotu na hutu da zaran ta dawo za mu kai su gaban kuliya domin a hukunta su in an same su da laifi” a cewarsa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *