Spread the love

Gwamnan Borno Ya Kai Ziyarar Bazata A Manyan asibitocin Jihar A Cikin Dare

Daga Alaji Engr Ibrahim Ismail

Da misalin karfe 1:00pm na dare Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya kai ziyarar bazata a babban asibitin zamani na Maiduguri  (Umaru Shehu Ultra Modern Hospital) da kuma asibitin kwararru na Maiduguri (Specialist Hospital).

Bugun farko Gwamnan ya fara da ziyarar a asibitin Umaru Shehu inda ya tarar babu wani Kwararren likita dake bakin aiki a asibitin cikin karrarun likitoci 10 da suke aiki a asibitin, a yayin da ya tarar da ma’akatan jinya guda 10 cikin 138 dake aiki a asibitin. Nan take Gwamnan ya kira duka Likitoci goma da suke aiki a asibitin ta waya amma bai same su ba.

Daga karshe Gwamnan ya garzaya Asibitin Kwararru na jihar inda can ma ya tarar da wasu Likitoci ba sa bakin aiki.

Tun lokacin da aka rantsar da shi Zulum ya bayyana cewa ba zai lamunci rashin zuwa aiki da ma’aikata suke yi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *